Za A Yi Taron Kasa Da Kasa Akan Mahangar Imam Khumaini Dangane Da Falasdinu

 A gobe Litinin ne dai za a bude taron karawa juna sani anan Tehran mai taken; Imam Khumaini da batun Falasdinu” wanda zai sami halartar

 A gobe Litinin ne dai za a bude taron karawa juna sani anan Tehran mai taken; Imam Khumaini da batun Falasdinu” wanda zai sami halartar masana na cikin gida da kuma waje.

Jawabin bude taro zai fito ne daga shugaban kungiyar kare hakkokin al’ummar Falasdinu, Hujjatul-Islam Muhammad Hassan Rahimiyan, haka nan kuma magajin garin Tehran Ali Ridha Zakani zai gabatar da jawabi.

 Bugu da kari a yayin wannan taron za a girmama jagororin gwgawarmaya da su ka yi shahada da su ka hada, Sahid Sayyid Hassan Nasrallah, shahid Isma’ila Haniyya, sai shahid Yahya Sinwar. Shi ma shugaban kungiyar Ansarullah ta Yemen Sayyid Abdulmalik Husi yana cikin wadanda taron na Tehran za karrama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments