Yemen ta sake harba makami mai linzami kan Isra’ila

Wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Yeman ya fada a yankuna Falasdinawa da aka mamaye. Yemen ta jima da take kai hare-hare

Wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Yeman ya fada a yankuna Falasdinawa da aka mamaye.

Yemen ta jima da take kai hare-hare kan Isra’ila a matsayin nuna goyan baya ga al’ummar Gaza dake fuskantar mamaya da ukuba da kisan kare dangi daga Isra’ila.

A cikin bayanin da ya yi bayan harin, babban jami’in gwagwarmayar Ansarullah ta kasar Yemen Nasr al-Din Amer, ya yi ishara da yadda gwamnatin Isra’ila ta yi watsi da kiran da kasashen Larabawa suka yi na neman zaman lafiya, ya kuma jaddada cewa hare-haren da ke faruwa a yankunan da aka mamaye, shi ne yare daya tilo da gwamnatin Isra’ila ke fahimta.

Hare-haren na Yemen sun yi matukar tasiri wajen durkusar da tattalin arzikin Isra’ila baya ga haifar da tsada sosai ga wasu kayayaki a Isra’ila, yayin da a daya bangaren kuma wasu hare-haren kan tsayar da al’amura a filin jirgin sama na Ben Gurion, mafi mahimmancin ga Isra’ila.

A martanin da ta mayar, Tel Aviv ta kara zafafa hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen.

Sai dai kuma dakarun na Yemen din sun lashi takobin ci gaba da kai hare-hare ba tare da kakkautawa ba, muddin gwamnatin kasar ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na kisan kiyashi da kuma kara tsananta hare-haren da take kai wa a zirin Gaza.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments