Yemen Ta Kore Wata Sabuwar Tuhumar Da Saudiyya Ta Yi Ma Ta Na Kai Wa Birnin Madina Hari

Tun da fari majiyar sojan Yemen ta kore labarin da Saudiyya ta rika watsawa a jiya Alhamisn a cewa; An kai wa cibiyar wutar lantarki

Shugaban majalisar koli ta siyasa a kasar Yemen Mahdi al-Mushaidh ya ce; Sabuwar tuhumar da Saudiyya ta yi wa Yemen na kai wa Madina hari, ba komai ba ne sai kame-kame saboda ta rasa yadda za ta yi.

Shugaban Majalisar koli ta siyasar kasar Yemen ya ce; Alhakin kai hari akan Makka da Madina yana wuyan Saudiyya.

Tun da fari majiyar sojan Yemen ta kore labarin da Saudiyya ta rika watsawa a jiya Alhamisn a cewa; An kai wa cibiyar wutar lantarki na birnin Madina mai alfarma.

Majiyar ta ce, ko kadan wannan riyawar da Saudiyyar ta watsa ba ta da tushe.

Kamfanin dillancin labarun “Saba” ya nakalto majiyar ta Yemen tana cewa; Sabuwar Karyar da Saudiyya ta kitsa saboda kara gishiri ne akan karyar baya da ta kirkira na cewa an kai wa Makka hari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted