Yemen Ta Kai Wa HKI Hari Da Makami Mai Linzami  Na  “Falasdinu 2”

Sojojin kasar ta Yemen sun sanar da kai wa yankin  Yafa hari da makami mai linzami da ya fi sauti sauri mai suna ” Falasdinu

Sojojin kasar ta Yemen sun sanar da kai wa yankin  Yafa hari da makami mai linzami da ya fi sauti sauri mai suna ” Falasdinu 2″, tare da tabbatar da cewa, ya fada inda aka harba shi.

A yau Asabar ne dai sojojin na Yemen su ka kai wa HKI harin da makami mai linzami mai tsananin sauri bisa abinda su ka kira da cewa; Mayar da martani ne akan ci gaba da yakin da ‘yan sahayoniya suke ci gaba da kai wa Gaza, da kuma jefa yankin cikin yunwa.

Kakakin sojan kasar Yemen, janar Yahya Sari, ya bayyana cewa; Makami mai linzamin da aka yi amfani da shi sunashi; “Falasdinu 2” kuma ya isa inda aka harba shi.

Janar Yahya Sari ya kuma ce: Dukkanin al’ummar musulmi ne suke da alhakin yin shiru akan abinda yake faruwa a Gaza, da kuma kin taimaka musu, sannan kuma ya ce: Ko ba dade-ko bajima, samamakon  yin shiru akan wuce gona da irin ‘yan sahayoniya zai isa cikin sauran kasashe.”

Janar Sari ya kuma ce; Gaza, tana kare dukkanin al’umma ne a wannan lokacin, domin taimaka mata shi ne ya fi dacewa da a tsumayi lokacin da sharri zai isa gidan kowa.”

Da safiyar yau Asabar ne dai  jiniyar gargadi ta kada a yankuna da yawa na HKI da su ka hada yankin Kudus, Tel Aviv da kuma ” “Dead Sea” bayan da aka harbo makami mai linzami daga kasar ta Yemen.

Makamin na dazu dai ne karo na uku da sojojin Yemen su ka harba a cikin sa’o’i 24.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments