Kasar Yemen ta sanar da cewa Amurka da ta sake kai wasu hare-haren a gundumar Hudaidah akan wani kamfani na auduga.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto majiyar Ansarullah ta kasar Yemen din tana cewa; Sojojin na Yemen sun kai hare-hare da makamai masu linzami har 18 akan jiragen ruwa na dakon jiragen yaki “USS Troman” hari.
Kakakin sojan kasar Yemen ne janar Yahya Sari ya sanar da kai hare-hare na martani akan jiragen yakin Amurka.
Tun daga ranar Asabar din da ta gabata ne dai jiragen yakin Amurka da na Birtaniya su ka rika kai wa Yemen hare-hare da sun yi sanadiyyar shahadar mutane da dama.
Yankunan da harin ya shafa sun hada biranen San’aa da kuma Sa’adah, sai kuma Hudaidai.
A gefe daya shugaban kungiyar Ansarullah ta Yemen Sayyid Abdulmalik Husi, ya ce: hare-haren ta’adanci wadanda sojojin Amurka da Burtaniya suka kai kan yankuna da dama a kasar ba za su hana mutanen kasar ci gaba da kare Falasdinawa a Gaza ba.
Haka nan kuma ya kara da cewa: Za su ci gaba da kai hare hare a kan jiragen HKI da na Burtaniya da na Amurkan, masu wucewa ta tekun malia kamar yadda ta bayyana tun farko.
Kungiyar Ansarullah ta kasar yemen dai ta tallafawa Falasdinawa a yakin tufanul Aksa wanda aka fara a ranar 7 ga watan octoban shekara ta 2023, har zuwa lokacin da aka tsagaita wuta tsakanin Falasdinawa a Gaza da HKI a ranar 19 ga watan Jenerun shekara ta 2025.
Mayakan “Jubhatun-Nusrah’ Na Kasar Syria Sun Kai Hari Akan Iyakar Kasar Leabnon
A jiya Lahadi ne dai kungiyar ta ‘yan ta’adda ta kai hare-hare akan iyakar Lebanon ta yankin Hermul
Ma’aikatar tsaron Syria ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta riya cewa; harin nata martani akan wani hari da aka kai a can cikin kasar wanda ta jinginawa HIzbullah, da kuma ya yi sanadiyyar mutumar jami’an tsaro uku.