Rahotanni da suke fitowa daga kasar Yemen sun ce, jiragen yakin Amurka da na Birtaniya sun kai hare-hare akan gundumar Hudaidah dake gabar ruwan tekun “Red Sea” a yammacin Yemen.
Wannan harin dai yana zuwa ne saboda matsawa San’aa ta dakatar da hare-haren da sojoji suke cigaba da kai wa manufofin HKI a karkashin taimakawa Gaza.
Jagoran kungiyar “Ansarullah” ta Yemen Abdulmalik Al-Husi ya sha nanata cewa ba za su daina kai irin wadannan hare-haren ba komai girman matsin lambar da za a yi musu, har sai in an kawo karshen yakin Gaza.