Hukumar kididdiga ta HKI ta bada sanarwan cewa yawan yahudawa da suke ficewa daga haramtacciyar kasar sun kara yawa.
Tashar talabijin ta Almayadeen na kasar Lebanon ta nakalto hukumar kididdiga na bada labarin cewa a shekara ta 2010 yawan masana wadanda suke da shahadar Jami’a da suka kaura daga kasar ya karu har ya kai kashi 46% sannan wannan adadin ya cilla sama a shekara ta 2023 bayan fara yakin tufanul aksa zuwa kashi 60.4 %.
Har’ila yau kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa a cikin yan shekarun da suka gabata, yahudawa masu ilmin Jami’a da dama sun bar kasar, saboda yanayin yaki wanda baya karewa a kasar.
Hukumar kididdiga na HKI a cikin yan kwanakin da suka gabata ta yada rahoto dangane da hijiran yahudawa, musamman daga cikin masu ilmi, wanda ya sa masu shigowa kasar sun ragu matuka a kan wadanda suke ficewa zuwa wasu kasashen duniya don neman inda ake zaman lafiya.
Bisa tsohon tsarin kididdiga na HKI, duk wani bayahude wanda ya share shekara guda a kasashen waje bai shiga HKI ko da na yan kwanaki ba to ana daukarsa a matsayin wanda yayi hijira daga kasar.
Amma a sabon tsarin gwamnatin yahudawan, ta ce duk wani bayahude wanda yayi kwanaki 275, wato kasa da shekara guda a kasashen waje, ko da yana zuwa kasar na yan kwanaki za’a lissafa shi daga cikin wadanda suka kaura daga kasar.
Bisa tsohon tsarin mutane dubu 16 suke ficewa daga kasar ba tare da sake dawowa ba, a ko wace shekara. Amma a cikin sabon tsarin an nuna cewa wannan adadin ya karu zuwa mutane dubu 36 a ko wace shekara ne suke ficewa ba tare da sun dawo ba.
Daga fara yakinnTufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 zuwa yanzu adadin yahudawa masu ilmi, wadanda suka hada da likitoci, inginiyoyi da sauransu ne suka fi ficewa daga kasar don duk inda suka je a duniya zasu sami aikin yi.