Hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kaiwa lardin Hudaida ya karu zuwa 74.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar gwamnmatin kasar ta Yemen na fadar haka a yau Jumma’a ta kuma kara da cewa dukkan mutanen da suka mutu a hare-haren jiragen yakin Amurka a cibiyar man fetur na Ras Isa a birnin Hudaida fararen hula ne. babu wani mayakin kungiyar Ansarulla ko guda a cikinsu.
Labarin ya kara da cewa jiragen yakin Amurka wadanda suka taso daga jiragen ruwa masu daukar jiragen sama na Amurka masu suna USS Harru Truman da kuma USS Carl a tekun red sea, sau kai hare kan ras Isa ne har sau biyu, hare na biyun ya fada ne kan ma’aikatan ceto da kuma yan kwana –kwana masu masu kashe wuta da cetun wadanda aka kaiwa hari na farko.
Majiyar Amurka ta bayyana cewa kayakin man fetur da ta kaiwa hari hukumar UNICEF ta MDD ce ta gina don haka kasar Yemen ba zata iya maida suba. Sannan kungiyar Ansarullah na samun kudaden tafiyar da kasar Yemen da su.