Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta kasar Lebanon ta bayyana cewa yawan mutanen da sojojin HKI suka kai ga shahada a kasar ya kai 3,754 sannan wasu 15,626 suka ji Rauni.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa mutane akalla 84 ne suka yi shahada a ranar Asabar da ta gabata kadai, sannan wasu 213 suka ji Rauni.
Labarin ya kara da cewa a birnin Beirut kadai mutane 29 suka yi shahada sannan wasu 67 suka ji Rauni.
Har’ila yau a lardin Ba’alabak-Helmer mutane 33 suka yi shahada sannan wasu 40 suka ji rauni.
Sai kuma kudancin kasar inda mutane 12 suka yi shahada sannan wasu 36 suka jirauni. A Nabatiyya kuma mutane 7 ne suka yi shahada sannan wasu 36 suka ji Rauni.
Har’ila yau rahoton ya kara da cewa ma’aikatan kiwon lafiya, kama daga likitoci da kuma ma’aikatan jinya, 222 ne suka yi shahada a yayinsa wasu 330 suka ji Rauni.