Yau Lahadi Ce Take Salla A Kasashen Larabawa Da Dama

A kasar Jordan gwamnatin kasar ta bada sanarwan cewa a gobe Litinin ce za’a gudanar da bukukuwan sallah karama bayan azumun watan Ramadan na kwanaki

A kasar Jordan gwamnatin kasar ta bada sanarwan cewa a gobe Litinin ce za’a gudanar da bukukuwan sallah karama bayan azumun watan Ramadan na kwanaki 30.

Muftin kasar ta Jordan Ahmed Hasanat a lokacinda yake bada sanarwan a jiya Asabar yace, ranar Litinin 31 ga watan Maris, ita ce ranar Sallah daya ga watan shawwal shekara ta 1446 Kmariya.

Kasashen Saudia, Qatar, UAE, Kuwait, Bahrain, Yemen, da kuma Palestine sun bada sanarwan cewa yau Lahadi ce sallah karama a kasashensu. Sai kuma kasashen Oman, Siriya da sun bayyana cewa gobe litinin ne salla karama.

A tarayyar Najeriya ma, sultan Sa’ad Abubakar na sokoto ya bada sanarwan sallah a yau Lahadi.

Majalisar koli ta al-amuran musulunci a Najeriya, karkashun shugabancin sultan Sa’ad Abubakar III ne ya bada wannan sanarwan a jiya da yamma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments