Yau Juma’a Ake Binne Shahid Ismael Haniyeh A Qatar

A wani lokaci yau Juma’a ne za’a binne shahid Ismael Haniyeh, shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas da Isra’ila ta kashe birnin Tehran. Kafin nan

A wani lokaci yau Juma’a ne za’a binne shahid Ismael Haniyeh, shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas da Isra’ila ta kashe birnin Tehran.

Kafin nan dai a jiya Alhamis akayi masa sallar jana’iza a birnin Tehran, inda jagoran juyin juya halin Musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya jagoranci sallar.

Haniyeh, wanda fitacce ne a fafutukar kare hakkin Falasdinawam ya dade yana gwagwarmaya kan kisan kare-dangin da Isra’ila take yi a Gaza.

Isra’ila ta dade da shan alwashin kashe Haniyeh da sauran shugabannin kungiyar Hamas.

Iran da kungiyar Hamas duk sun sha alwashin mayar da martini mai zafi kan kisan na Ismael Haniyeh.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments