Yansanda A Kasar Turkiyya Suna Ci Gaba Da Fafatawa Da Yan Adawa A Birnin Istambul

Yansanda a kasar Turkiyya suna ci gaba da fafatawa day an adawa masu goyon bayan magajin garin birnin Istambul Ekram Imam oglu. Tashar talabijin ta

Yansanda a kasar Turkiyya suna ci gaba da fafatawa day an adawa masu goyon bayan magajin garin birnin Istambul Ekram Imam oglu.

Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa magajin garin na birnin Istambul yana daga cikin fitattun masu adawa da gwamnatin Urdugan, sannan a halin yanzu jami’an sharia a kasar sun bada sanarwan cewa sun kammala bincike a kansa, kuma nan ba da dadewa ba zasu gurfanar da shi a gaban kotu don fuskantar shari’a.

A ranar laraban da ta gabat ce gwamnatin kasar Turkiya ta bada umurnin kama Ekram Imam oglu magajin garin birnin Istambul tare da zarginsa da cin hanci da rashawa da kuma ayyukan ta’addanci. Wanda ya musanta hakan a yanke.

Har’ila yau masu gabatar da shari’a a kasar sun bukaci a ci gaba da tsare magajin garin har zuwa lokacinda za’a fara shari’arsa a cikin yan kwanaki masu zuwa. Tun ranar laraban da ta gabace yan sanda a birnin istambul da kuma wasu birane a kasar suke fafatawa da dubban daruruwan magoya bayan Imam oglu wadanda suke bukatar a sake shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments