Kungiyar M 23 da take samun goyon bayan Rwanda tana kara karfafa ikonta a garin Goma dake gabashin jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da su ka hada da filin saukar jiragen sama, kamar yadda MDD ta sanar.
A yau Laraba shugaban kasar Rwanda da gwmanatinsa take goyon bayan ‘yan tawayen kungiyar M23, ya yi kira da a tsagaita wutar yaki.
Da safiyar yau Laraba an sami dawowar kwanciyar hankali a cikin birnin na Goma bayan da a jiya mazaunansa fiye da miliyan biyu su ka kasance a cikin zullumi da fargaba.
Mazauna birnin na Goma sun fadawa kamfanin dillancin Labarun (AP) cewa ‘yan tawayen kungiyar ta M 23 ne suke rike da mafi yawancin birnin.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai kungiyar ta M 23 ta sanar da cewa ta kame wannan birnin na Goma bayan mayakanta sun dauki kusan mako daya suna matsawa kusa da shi.
Kungiyar M 23 daya ce daga cikin kungiyoyin tawaye 100 da ake da su a cikin kasar ta jamhuriyar Demokradiyyar Congo da kowace daya daga cikinsu take son shimfida iko a cikin yankunan da ake da ma’adanai.
Ita dai kasar DRC tana da dimbin arzikin ma’adanai da suke kwance a karkashin kasarta, da ya sa kasashen makwabta da kuma na nesa suke taimakawa wasu daga cikin kungiyoyin ‘yan tawaye saboda su yi kaso mu raba da arzikin wannan kasar.
Tun da kasar ta Sami ‘yanci daga kasar Belgium, ba ta sami zaman lafiya ba har zuwa yanzu.