Kamfanin dillancin labarun “Anatoli” na Turkiya ya ambato cewa; Ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Nijar Mohamed Toumba ne ya bayar da labarin cewa, mutane da dama sun kwanta dama sanadiyyar harin da a ka kai wa masu salla a garin Fonbita dake yankin Kokorou.
Rahotannin sun tabbatar da cewa adadin masu sallar da su ka yi shahada sun kai 57wasu 13 kuma su ka jikkaya.
Jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da cewa kungiyar “Da’esh’ ta ‘yan ta’adda ta sanar da cewa ita ce ta kai wannan harin.