Kungiyar ‘yan jarida ta Falasdinawa ta sanar da cewa; sojojin mamayar HKI sun kashe ‘yan jarida 44 da suke a cikin sansanonin ‘yan hijira mabanbanta a yankin Gaza.
Sanarwar ta ce, wannan adadin, yana a karkashin jumillar ‘yan jarida 254 da su ka yi shahada a tsawon lokacin yakin da ya fara daga watan Oktoba na 2023, zuwa watan Oktobar wannan shekarar ta 2025.
Kwamitin dake kare ‘yancin aikin jaridar dake karkashin kungiyar ‘yan jaridar ta Falasdinawa, ya ce; Kashe ‘yan jarida da HKI take yi wani shiryayyen tsari ne da ya hada kai hare-hare akan sansanon ‘yan hijira da suke a kusa da asibitoci da sauran cibiyoyin da hukumar ‘yan hijirar Falasdinawa ta MDD, Unrwa take kula da su.
A gefe daya wani jimi’in kungiyar gwgawarmayar Faladinawa ta Hamas, Isma’ila Ridhwan, ya ce, mafi yawancin ‘yan jaridar dai an kashe su ne a lokacin da suke kan ganiyar gudanar da ayyukansu na nunawa duniya mawuyacin halin da al’ummar Falasdinu suke ciki.