‘Yan Gwgawarmaya Sun Kashe Sojojin HKi 4 A Gaza

Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa 4 daga cikin sojojinsu na mamaya sun halaka a sanadiyyar fashewar wata nakiya da aka dasa wacce ta

Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa 4 daga cikin sojojinsu na mamaya sun halaka a sanadiyyar fashewar wata nakiya da aka dasa wacce ta tashi da daya daga cikin motocinsu a Gaza.

Majiyar ‘yan sahayoniyar ta ce,baya ga sojojin 4 da su ka halaka a yau Alhamis, an kuma samu wasu 8 da su ka jikkata lokacin da motar Hommer ta daukar sojoji da aka dasawa nakiya ta fashe da su.

Kafafen watsa labarun na ‘yan sahayoniya sun bayyana abinda ya faru da cewa: Yana da tsananin ciwo”, sannan kuma su ka kara da cewa, lamarin ya faru ne a yankin da ake dauka cewa yana da aminci.

A wani gefen, kungiyar ” Kata’ibul-Mujahidin” ta sanar a yau Alhamis cewa; mayakanta sun harbi tankar yaki ta ” Mirkava” da makamin “Sa’ir” a unguwar “Zaytun”, ya kuma same ta da kyau.

Tun daga lokacin da sojojin mamaya su ka fara kai sabbin hare-hare da zummar sake mamaye yankin Gaza, ‘yan gwgawarmaya suke kara kaimi wajen kai musu hare-hare.

Yakin da HKI ta shelanta akan Gaza ya cika kwanaki 712, wanda yake cike da kisan kiyashi da na kare dangi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted