‘Yan gwagwarmayar Siriya Sun Fara Kai Hare-Hare Kan Sojojin Mamayar Isra’ila

‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun

‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila

Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun fuskanci bude wuta daga yankin kudancin Siriya, wanda kungiyar gwagwarmayar al’ummar Siriya ta yi ikirarin kai harin wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da sojojin mamaya suka kutsa kai cikin yankunan Siriya bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad.

Sojojin mamayar Isra’ila sun tabbatar da kai wani farmaki kan rundunar sojinsu a kudancin Siriya a jiya Juma’a.

A jiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kai farmaki kauyen Taranja da ke yankin Quneitra a kudu maso yammacin kasar Siriya, inda suka kame mutane biyu.

Wakilin gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya bayyana cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun bude wuta kan sojojin mamayar Isra’ila a yankin Quneitra, yana mai cewa: Wannan shi ne karon farko da aka kai hari kan sojojin mamayar Isra’ila bayan watanni biyu suna yawo cikin ‘yanci a yankunan kasar Siriya.

Dan rahoton ya yi nuni da cewa: Ko wannan hari shi ne mafarin yunkurin ‘yan gwagwarmaya nuna rashin amincewarsu da matakan da sojojin mamayar Isra’ila suka dauka kan kasar Siriya na wuce gona da iri musamman ruguza duk wasu sansanonin soji da cibiyoyin binciken ilimin dabaraun yaki da wasu muhimman wuraren tsaro a kasar ta Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments