Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah da ke kasar Lebanon tana ci gaba da kai farmaki kan wuraren da aka jibge sojojin makiya ‘yan mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a kan iyakar Lebanon da Falasdinu, don nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu da suke ci gaba da tsayin daka a Zirin Gaza da kuma goyon bayan gwagwarmayar kare kai mai daraja da kima gami da jajurcewar neman ‘yanci, da kuma mayar da martani ga ‘yan sahayoniyya masu kai hare-haren wuce gona da iri kan al’ummun Lebanon.
A halin da ake ciki dai, da misalin karfe 01:00 na safiyar yau alhamis ne ‘yan gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi suka kai wasu jerin farmaki kan Bayadh Balida da manyan bindigogi tare da tarwatsa wurin kai tsaye.