‘Yan Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Yi Watsi Da Bukatar Hukumar Falasdinawa

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa da suke sansanin ‘yan gudun hijiran Jenin sun yi fatali da kiran mika makamansu Wani jigo a bataliyar Jenin ya jaddada cewa:

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa da suke sansanin ‘yan gudun hijiran Jenin sun yi fatali da kiran mika makamansu

Wani jigo a bataliyar Jenin ya jaddada cewa: Sun dakatar da duk wasu shirye-shiryen da suka amince da su da suka shafi kawo karshen rikicin sansanin Jenin saboda shawarar siyasa da shugaban hukumar cin Gashin kan Falasdinawa Mahmoud Abbas ya yanke.

Jami’in ya bayyana a cikin sanarwar manema labarai cewa: A duk lokacin da suka samu sakonni daga manyan jami’an hukumomin Falasdinawa, to za a ji cewa ne mafitar da ta fi dacewa gare su ita ce kodai su shirya fuskantar ci gaba da hare-haren soji, ko kuma mayakan gwagwarmaya su mika kansu da makamansu.

Yana mai jaddada cewa: Wannan zabin ba abu ne da ba za su amince da shi ba, ya kuma kara da cewa, “duk wata tattaunawa da za a yi don kawo karshen rikicin da ke faruwa a sansanin Jenin, tilas ne a tsaya kan sharadin rashin neman ajiye makamai daga ‘yan gwagwarmaya, kuma a shirye suke su tattauna kan komai, amma banda batun ajiye makamai, a cewarsa. Kamar yadda jaridar Hurriya ta ruwaito.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments