Kungiyar gwagwarmaya ta kasar Iraki ta sanar da kai hari a jiya Talata akan manufofin HKI ta hanyar amfani da jirage marasa matuki.
Sanarwar ta kuma ce, sun kai wadannan hare-haran ne saboda yadda ‘yan sahayoniyar suke cigaba da kashe mata da kananan yara a Falasdinu da Lebanon.
Kungiyar gwagwarmayar ta Iraki ta kuma jaddada cewa za ta cigaba da kai wa manufofin HKI hare-hare har zuwa lokacin da za a kawo karshen yakin Gaza da Lebanon.
Tun a farkon yakin Gaza ne a 2023 ne ‘yan gwgawarmaya daga Irakin su ka fara kai wa manufofin HKI hare-hare ta hanyar amfani da jirage marasa matuki da kuma makamai masu linzami dake cin dogon zango.