Dokar Soji : Ministan Tsaron Koriya Ta Kudu Ya Yi Murabus

Ministan tsaron Koriya ta Kudu Kim Yong-hyun ya ba wa ‘yan kasar  hakuri a ranar Laraba nan tare da mika takardar murabus dinsa bayan gazawar

Ministan tsaron Koriya ta Kudu Kim Yong-hyun ya ba wa ‘yan kasar  hakuri a ranar Laraba nan tare da mika takardar murabus dinsa bayan gazawar shugaban kasar Yoon Suk Yeol na kafa dokar soji.

“Na yi nadama sosai tare da daukar cikakken alhakin rudani da damuwa da jama’a suka shiga saboda dokar, kuma kan na mika wa shugaban kasa takardar murabus,” in ji Mista Kim a cikin wata sanarwa.

Tunda farko dai’Yan adawa a majalisar dokokin Koriya ta Kudu sun sanar da gabatar da bukatar tsige shugaban kasar Yoon Suk-yeol, bayan yunkurin da ya yi na kafa dokar ta baci.

Daga baya ‘yan majalisar za su yanke shawarar ranar da za a kada kuri’a kan wannan kudiri, wanda zai iya gudana a ranar Juma’a mai zuwa, kamar yadda jam’iyyun adawar suka sanar yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa yau Laraba.

Shi dai Shugaba Yeol na kasar Koriya ta Kudu ya kafa dokar ta-baci lokacin wani jawabi da ya gabatar kai tsaye ta kafofin yada labarai rarar Talata, lamarin da ya fusata ‘yan kasar da dama.

Rahotannin sun ce matakin ya sanya masu zanga zanga mamaye majalisar dokokin kasar bayan sanar da matakin.

Shugaban kasar dai ya zargi ‘yan adawa da suka mamaye majalisar dokokin kasar da yin sako-sako game da batun kasar Koriya ta Arewa duk da yadda take zama barazanar tsaro ga kasarsa.

Shugaban ya ce ya kafa dokar ta-bacin ne domin magance ‘yan kanzagin Koriya ta Arewa da tabbatar da kundin tsarin mulkin kasar game da ‘yancin fadin albarkacin baki.

To saidai majalisar dokokin kasar ta kada kuri’ar watsi da matakin lamarin da ya jefa kasar cikin wata dambarwar siyasa.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments