Yamen Ta yi Tir Da Gum Da Baki Da MDD Ta Yi

gwamnatin kasar yame ta yi tir da gum da baki da majalisar dinkin duniya ta yi na yin gum da baki da harin da saudiya

Gwamnatin kasar yamen ta yi  tir da matakin da majalisar dinkin duniya da sauran kungiyoyin masu fada a ji na duniya suka dauka game da gum da baki da suka yi  kan ci gaba da kai hare hare da kasar saudiya ke yi kan alummar kasar yamen da kuma  killaceta

A cikin wani bayani da Ma’aikatar harkokin wajen kasar Yamen ta fitar ta nuna cewa sojojin kasar Sauidya na ci gaba da kai hare hare kan fararen hula da sauran mutanen gari da muhimman wuraren more rayuwar alumma , inda ta fara tun daga shekarar da ta gabata,

Ma’aikatar tayi tir da hare haren da kasar Saudiya take kai wa kan fararen hula da wuraren da ba na soji ba. wanda hakan ya sabama dokokin kasa da kasa, musamman jarjejeniyar janaiba ta 4 ta shekara ta 1949 da kuma kudirin da aka fitar na daya na shekara ta 1977

A baya bayan nan kasar saudiya ta kai hari kan gidajen makwabta a garin maqban dake yamma maso gabashin lardin ta’izz kuma ta kashe mutane 9 da suka hada da mata da yara kanana tare da jikkata wasu guda 16.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted