Da safiyar yau Laraba Yahudawa ‘yan share wuri zauna sun kutsa cikin masallacin kudus a karkashin kariyar jami’an tsaron ‘yan sahayoniya, tare da yin ayyukan bautar yahudanci a ciki.
Wannan kutsen dai yana zuwa ne a daidai lokacin da sojojin HKI suke ci gaba da kai wa Falasdinawa hare hare a cikin yankuna mabanbanta na Gaza da yammacin kogin Jordan.
Rahotanni da suke fitowa daga Falasdinu sun ce ya zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada sun haura 18. Daga cikin wadanda su ka yi shahadar da akawi Fursunonin da aka ‘yanto su a musayar fursunoni tsakanin Hamas da HKI.
A yankin Khalil sojojin HKI sun kutsa cikin kauyen Ummul-Khair tare da kame mutane 8 bayan yin kutse a cikin gidajensu.
Haka nan kluma sojojin mamayar sun kama wasu matasa biyu a garin “Tuba” wanda yake a Khalil.
Wasu Falasdinawan 3 sun yi shahada a yau Laraba a wurin karbar abinci, bayan da sojojin HKI su ka bude musu wuta.
A cikin asibitocin yankin na Gaza an kai gawawwakin shahidai 16 daga cikinsu da akwai 16 da su ma masu neman abinci ne.