Wasu gungun yahudwa yan share wuri zauna sun bankawa wani masallaci wuta a gabar yammacin kogin jodan da Isra’ial ta mamaye inda ya lalata cikin masallacin , wannan shi ne hari na baya bayan nan da yahudawan yan share wuri zauna suka kai kan Alummar faladinu duk da yar jejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma.
Kamfanin dillancin labaran falasdinu WAFA ya bayyana cewa an kai wannan harin ne kan masallacin hajja hamida dake arewa maso yammacin birnin salfti da safiyar yau alhamis,
ya kara da cewa mazauna yanki sun kadu sosai lokacin da suka ga yahudawan sun bankawa masallacin wuta tare da watsa wasu abubuwan fashewa a kofar masallacin, haka zalika sun rubuta taken nuna kin jinin musulmi da larabawa a jikin bangon masallacin,
shugaban kungiyar gwagwarmyar kwatar yancin falasdinu CRRC Muayyad shaaban ya fadi cewa a ranar 5 ga watan nuwamba sojojin Isra’ila sun kai hare hare 1584 a fadin yankin gabar yammacin kogin Jodan wanda ya hada da cin zarafi kai tsaye rushe gidaje da kuma tunbuke bishiyoyin Zaitun,
Kotun duniya mai hukumta laifukan yaki ta sanar da ci gaba da fadada gine gine matsunguunen yahudawa yan share wuri zauna da cewa ya sabama doka, don haka ta bukace ta da ta rusa dukkan gine gine a gabar yammacin kogin jodan da kuma gabashin birnin Qudus,