Rahotannin cibiyoyin kididdiga a HKI sun ambaci cewa, ana ci gaba da samun yin hijirar yahudwa zuwa waje wanda shi ne mafi girma a cikin shekaru da dama.
Jaridar “Ma’ariv” ta ambato wani makwararre a fagen kididdiga yana cewa; Shekarar 2024 ta fuskanci ficewar mutane masu yawan gaske daga “Isra’ila” saboda yakin da ake yi a Gaza. Haka nan kuma ya ce, wannan shi ne karo na hudu a cikin shekaru masu yawa da ake yin hijira daga Isra’ila.
Bugu da kari ya ce, baya ga yahudawa da akwai ‘yan hijira da dama da suke ficewa da hakan yake da jan hankali sosai.
Haka nan kuma ya ambaci wasu daga cikin dalilan da su ka Sanya ake yin hijira da su ka hada da rashin tsaro,da kuma tabarbarewar tattalin arziki.
A jiya Laraba ne dai cibiyar kididdiga ta ‘yan sahayoniya ta fitar da rahoto wanda ya bayyana cewa; a cikin shekarar da ta gabata kawai adadin wadanda su ka yi hijira daga “Isra’ila” sun kai 79,000.
Rahoton na jiya laraba ya kuma yi ishara da cewa; Adadin wadanda ake kira da ‘yan Isra’ila sun kai miliyan 10, da budu 148. Daga cikin wannan adadin da akwai yahudawa miliyan 7 da dubu 758, da su ne kaso 78.5 %. Su kuwa wadanda ba yahudawa ba sun kai miliyan biyu da dubu dari da talatin wato kaso 21.5%.Haka nan kuma da akwai ‘yan kasashen waje da su ka kai 260,000.Fiye da bakin haure ne su ka fice daga wannan Haramtacciyar kasa.
Kisan kiyashin da HKI ta shelanta akan Gaza ya durkusar da tattalinb arzikinta.