WTO Ta Yi Gargadi Akan Karin Kudin Fito Na Amurka

Kungiyar kasuwanci ta duniya ta bayyana cewa, za a sami raguwar hajar da za a yi kasuwancinta a duniya  da kaso 0.2% saboda Karin kudin

Kungiyar kasuwanci ta duniya ta bayyana cewa, za a sami raguwar hajar da za a yi kasuwancinta a duniya  da kaso 0.2% saboda Karin kudin fito da Amurka ta yi.

Rahoton kungiyar kasuwancin ta duniya wanda aka fitar da shi a ranar Litinin din da ta gabata ta gina shi ne akan yadda tafiyar kasuwanci za ta kasance daga 2025-2026, wanda aka tsammaci zai rika samun bunkasa, sai dai kuma Karin kudaden fito da Donald Trump ya yi, ya sa kungiyar ta sauya hasashen da ta yi a baya.

Cinikayya ta kayayyaki zai ta yi baya da kaso 1.5% idan har Donald Trump din ya yi aiki da sabuwar siyasar tasa ta haraji.

Shugaban na Amurka ya dakatar da aiki da sabon salon haraji na tsawon kwanaki 90, domin bai wa kasashe 70 na duniya damar sauya yadda suke cinikayya da Amurka. Karin da Trump din ya yi wa kayan China ya kai kaso 145%, yayin da ya dan saukaka shi akan kasashen Canada da Mexico.

Babbar daraktar kungiyar kasuwancin ta duniya Ngozi Okonjo -Iweala ta sanar da cewa; Duk da cewa an sami tsaikon aiwatar da sabon haraji, amma duk da haka da akwai rashin tabbaci a kasuwannnin na duniya da hakan a kanshi yake a matsayin wani cikas na ci gaba.

Wannan dai ba shi ne karon farko da kungiyar ta kasuwanci ta duniya tare da Asusun Bayar Da Lamuni su ka yi gargadi akan yadda za a sami koma baya a fagen kasuwanci da cinikayya a duniya ba, saboda matakin na kasar Amurka na Karin harajin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments