WHO Za Ta Bai Wa Najeriya Magungunan Cutar Kuturta

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za ta aika da magungunan cutar kuturta zuwa Najeriya. Wannan dai na zuwa ne bayan jinkirin da aka samu

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za ta aika da magungunan cutar kuturta zuwa Najeriya.

Wannan dai na zuwa ne bayan jinkirin da aka samu na gwaje-gwajen da hukumar ke gudanarwa, lamarin da ya jawo dubban masu fama da cutar ciki har da yara ba su samu magungunan da suka kamata na kare cutar ba.

Kakakin hukumar ta WHO ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewar, an samu ƙarancin maganin cutar ta kuturta a Nijeriya.

Ya ce hukumar ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta miƙa buƙatar ganin an samu izinin shigar da maganin cikin ƙasar akan lokaci, kuma a watan Janairu aka amince da hakan.

Nijeriya wadda ita ce ƙasar Afirka da ta fi yawan jama’a na bayar da rahoton samun aƙalla mutum 1,000 da cutar kuturta a duk shekara, wadda cuta ce da ke kama fatar jiki da jijiyoyi da idanu.

Ana iya magance cutar bayan shan magani na wani lokaci, amma idan ba a shan magani, cutar na ƙaruwa, idan take jawo gyambo da kuma nakasa kamar makanta da shanyewar rabin jiki.

Haka kuma, masu fama da cutar na fuskantar hantara da tsangwama a cikin al’umma.

Sai dai magungunan da Nijeriya take da su na cutar sun ƙare a farkon shekarar 2024 sakamakon jinkirin da aka samu na sabbin dokokin cikin gida da aka samar na gwaje-gwaje kan magungunan da ake shigar da su cikin ƙasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments