WFP: Yara Miliyan 11 Na Fama Da Karanci Abinci A Nijeriya

Wani sabon rahoto da hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta fitar a Nijeriya, na ishara da cewa mutum miliyan 11 ne a fadin

Wani sabon rahoto da hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta fitar a Nijeriya, na ishara da cewa mutum miliyan 11 ne a fadin jihohi shida na Arewa maso Gabas da Arewa maso Yammacin Nijeriya ke fuskantar matsalar karancin abinci a shekarar 2025.

Kazalika, rahoton ya danganta matsalar da rashin tsaro da ake ci gaba da fuskanta, da hauhawar farashin kayan abinci da man fetur, da bala’in yanayi, da kuma matsugunan jama’a, ya sa miliyoyin mutane ke fafutukar samun abinci mai gina jiki.

Rahoton UNICEF ya kara bayyana cewa yara ‘yan kasa da shekaru biyar a Nijeriya, kusan miliyan 11, na fama da matsanancin rashin abinci, wanda hakan ya sa kashi 50 cikin 100 na ka fuskantar barazana ga rayuwarsu.

Rahoton ya bayyana rashin wadataccen abinci mai gina jiki, da wahalhalun tattalin arziki na iya zama ummul-haba’isin muhimman abubuwan da ke haifar da rashin abinci ga yara.

A cikin 2024 kadai, kungiyar (MSF) ta ce ta yi wa yara sama da 300,000 maganin tamowa, doriyar kashi 25 cikin 100 daga 2023.

Daga cikin wadannan kaso, 75,000 na bukatar kulawar rashin lafiya mai tsanani, yayin da 250,000 aka basu kulawa ta hanyar shirye-shiryen sama musu lafiya a fadin jihohi bakwai: Borno, Bauchi, Katsina, Kano, Sokoto, Zamfara, da Kebbi.

Wakilin kungiyar ta MSF na kasa Dr Simba Tirima ya shaida wa LEADERSHIP cewa kungiyar agajin ta lura da yadda ake samun karuwar masu dauke da cutar, wanda ya zarce shekarun baya a duk cibiyoyin kula da lafiyarsu.

“Rashin abinci mai gina jiki na kara ta’azzara, tare da samun karin yara a wuraren da ake kula da su,” in ji Dr Tirima.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments