Washington Post: Shirin Trump Na Kai Sojojin Gaza Yana Fuskantar Matsala

Jaridar Washington Post ta buga rahoto akan Shirin Donald Trump na aikewa da sojoji zuwa Gaza, tare da cewa tana fuskantar matsala, domin har yanzu

Jaridar Washington Post ta buga rahoto akan Shirin Donald Trump na aikewa da sojoji zuwa Gaza, tare da cewa tana fuskantar matsala, domin har yanzu ana Magana akan yadda za a raba ‘yan gwgawarmaya da makamansu.

Jaridar ta ci gaba da cewa; Da akwai damuwa a cikin manyan biranen kasashen duniya danagne da yiyuwar a bukaci sojojin da za a aika su yi amfani da karfi akan Falasdinawa.

A ranar 17 ga  watan Nuwamba ne dai kwamitin tsaro na MDD ya fitar da kuduri na amincewa da Shirin da Trump yake da shi akan abinda ya kira zaman lafiya a Gaza.

Kasar Indonesia ta yi alkawalin aikewa da sojojin da za su kai 20,000 domin aikin tabbatar da zaman lafiya. Sai dai kuma kasar tana bukatar ganin an rage yawan aikin da sojojin za su yi.

Ita ma kasar Azerbaijan wacce ta yi alkawalin aikewa da sojoji zuwa Gaza, tana yin bitar abinda ya kamata su yi.

Sai dai har yanzu babu wata kasar larabawa wacce ta yi alkawalin aikewa da sojoji zuwa Gaza a karkashin Shirin an Trump.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments