Wani Mummunan Harin Isra’ila Ya Kashe Mutane Da Dama A Gaza

Rahotannida ga Falasdinu na cewa wani sabon harin  Isra’ila ya yi sanadin rayukan Falasdinawa da dama a yankin Zirin Gaza a daidai lokacin da ‘yan

Rahotannida ga Falasdinu na cewa wani sabon harin  Isra’ila ya yi sanadin rayukan Falasdinawa da dama a yankin Zirin Gaza a daidai lokacin da ‘yan mamaya ke ci gaba da kai hare-hare kan yankin da aka yi wa kawanya.

Kafofin yada labaran cikin gida sun ambato majiyoyin kiwon lafiya na cewa, an samu asarar rayuka bayan da sojojin Isra’ila suka kai hari da makamai masu linzami a yankuna daban-daban a arewaci da tsakiyar Gaza yau Laraba.

Majiyar ta ce harin ya kuma yi sanadin jikkatar Falasdinawa 27 a yankunan arewacin kasar.

Da sanyin safiya ne sojojin mamaya na Isra’ila suka kai harin bam a wani gini da ke Beit Lahiya kusa da Asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Gaza.

Harin da aka kai a yankin ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 28 da suka hada da mata da kananan yara, tare da yiyuwar adadin wadanda suka mutu ya karu yayin da aka ce ginin benaye na dauke da mutane akalla 30 da suka rasa matsugunansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments