Search
Close this search box.

Wani Makami Mai Linzami Daga Yemen Ya Fada Tsakiyar Isra’ila

Rundunar sojin Isra’ila ta yi ikirarin cewa makami mai linzami da aka harba daga kasar Yemen ya fada a tsakiyar kasar a yankunan da aka

Rundunar sojin Isra’ila ta yi ikirarin cewa makami mai linzami da aka harba daga kasar Yemen ya fada a tsakiyar kasar a yankunan da aka mamaye, inda akalla mutum tara suka jikkata.

 Rahotanni sun ce tsarin Iron Dome na kariya daga hare-hare saman na Isra’ila ya gaza wajen dakile harin.

Makamin ya sauka ne a kudu maso gabashin birnin Tel Aviv da kuma tashar samar da wutar lantarki ta Gezer a safiyar Lahadin nan.

Hotunan bidiyo da hotuna da aka yada ta yanar gizo sun nuna hayaki na tashi daga ciyawar da makamin ya fada bayan da sojojin Isra’ila suka yi yunkurin harbo shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments