Fitaccen lauya dan kasar Ghana Mr. Mahmud Mudi ya bayyana cewa, sammacin kamo Fira ministan Isra’ila da kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ta fitar abu ne mai muhimmanci.
A wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarun Iran na “ Iran Press” Mahmud Mudi ya ce, saboda kotun manyan laifukan ta kasa da kasa tana da hurumin fitar da sammacin kamo kowane mutum, abinda ta yi din game da Netanyahu daidai ne.
Har ila yau Mahmud Mudi ya ce; Natenyahu yana daukar kansa a matsayin wanda ya fi karfin doka,to amma wannan matakin da aka dauka zai taka masa birki akan abubuwan da yake yi a gabas ta tsakiya, domin yana da masaniya akan cewa duk abinda zai aikata, hakan zai sa siyasarsa ta sami tsaiko.
Lauya Mudi ya kuma ce; Da akwai rashin adalci mai yawa da yake faruwa a cikin siyasar kasa da kasa, ta yadda wasu mutane suke jin cewa sun fi wasu matsayi da daraja,saboda kawai wasu manyan kasashe masu karfi suna tare da shi.