Amurka ta sake kai wani hari ta sama kan babban birnin kasar Yemen, Sana’a, inda ta kashe fararen hula akalla 12 tare da jikkata wasu fiye da 30 na daban.
Mummunan harin na Amurka an kai shi ne a wata kasuwa mai cike da cunkoson jama’a a unguwar al-Farwa da ke gundumar Sha’ub a safiyar ranar Litinin.
Ana fargabar adadin wadanda suka mutu zai karu yayin da mutane da dama ke makale a karkashin baraguzan gine-gine da aka wargaza a harin.
A gefe guda kuma, Amurka ta kai hare-hare a yankunan lardin Sa’ada, a arewa mai nisa na kasar, da tsakiyar Ma’rib, da yammacin Hudaydah.
Dama kafin hakan a ranar Lahadi, Amurka ta kai wasu hare-hare ta sama a Yemen, ciki har da Sana’a, inda aka kashe akalla uku.
A cikin watan da ya gabata ne dai sojojin Amurka suka zazafa kai hare-hare a kasar Yemen, bisa ikirarin dakile hare-haren kungiyar Ansarullah dake kai farmakin goya bayan falasdinu kan jiragen ruwa masu alaka da Isra’ila.
Fiye da mutane 200 ne aka kashe a harin da Amurka ta kai kan Yemen tun cikin watan Maris.