Wani dan majalisar dokokin kasar Rasha ya bayyana cewa kasashen yamma basa son samuwar kungiyar tattalin arziki ta BRICS saboda suna son su ci gaba da zama shuwagabannin duniya a kan kowa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Konstantin Kosachev yana fadar haka a birnin Mosco ya kuma kara da cewa, a cikin sabuwar duniya da muke cikin zamanin shugabancin wasu yan tsiraru a kasashen yamma ya wuce, daga yanzun mafi yawan kasashen duniya suna bukatar a gudanar da harkokin tattalin arziki, siyasa da zamantakewa a duniya tare, ba tare da nuna bambanci ba.
Kosachev ya kara da cewa mafi yawan kasashen duniya a halin yanzu suna bukatar a dama dasu a harkokin tafiyar da duniya, a mutunta ra’ayinsu, a kuma yi aiki tsakanin kasashen duniya ta hanyar musayar ra’ayi da kuma gamuwa a kan dukkan manya manyan al-amura da suka shafi tafiyar da duniya.
Kungiyar BRICS dai an kafata ne a shekara ta 2000 tsakanin kasashen Barazil, Rasha, Indiya, China da kuma Afirka ta kudu. Kuma manufar kungiyar itace samar da sabuwar duniya wacce kasashen duniya zasu sami zabi a cikin al-amuran tafiyar da duniya. A cikin wannan shekarar ne kungiyar ta tattalin arziki ta BRICS ta kara yawan kasashen kungiyar zuwa 11.
Ana kuma saran nan gaza zata zama abokiyar hamayyar kasashen yamma a cikin al-amura da dama a harkokin tafiyar da duniya.