Anicen Ekane dan adawa na jam’iyyar African Movement for New Independence yana daga cikin fitattun yan siyasa a kasar Kamaru, kuma yana goyon bayan Issa Chiroma a zaben shugaba kasa wanda aka gudanar a kasar a cikin watan Octoban da ya gabata.
Issa Chiroma dai ya shelanta cewa shi ya lashe zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a cikin watan Octoban da ya gabata.
Jami’an tsaro sun yi dirar mikiya kan masu goyon bayan Chiroma, kuma sun kashe mutane da dama sun kuma kama wasu Anicen Ekaney ana daga cikin wadan da aka kama a birnin Duala a ranar 24 ga watan Octoba. Kuma Ekane ya zargi jami’an tsaro da kwace maganin Oxigen dinsa, wanda ya jefa rayuwarsa cikin hatsari, sannan daga karshe lawyansa ya bada sanarwan mutuwarsa a yau Litinin a tsare a hannun jami’an tsaron kasar. Kafin haka jam’iyyarsa ta bada sanarwan cewa, kwace maganinsa wanda Jami’an tsaro suka yi zai jefa rayuwarsa cikin hatsari.