Wakilan kasashe sun fice daga zauren MDD, gabanin jawabin Netanyahu

A yayin da shugabanni da wakilan gwamnatocin kasashe ke ci gaba da jawabi a babban zauren MDD, firaministan Isra’ila shi ma ya gabatar da nasa

A yayin da shugabanni da wakilan gwamnatocin kasashe ke ci gaba da jawabi a babban zauren MDD, firaministan Isra’ila shi ma ya gabatar da nasa jawabi da yammacin yau, saidai ya ci karo da ihu da kuma ficewa daga zauren daga wasu wakilan kasashe dake zamne a zauren.

Jakadun kasashen Musulmi, Larabawa, Afrika da Latin Amurka ne suka ficewa, sannan wasu daga Turai suka bi su.

Amurka ce da wasu kawayenta daga yankin Pacific, da wasu kasashen kalilan ne suka rage a zauren.

An kuma rawaito yin zanga zanga a birnin New York ta goyan bayan falasdinu da kuma neman kawo karshen yakin Gaza.

Netanyahu ya kwashe sama da mintina 45 yana jawabi inda ya tabo batutuwa da dama, a sahun gaba yakin kasarsa da Iran na kwanaki 12.

Netayanhun ya kuma tabo babun yakin kisan kare dangin da yake jagoranta a Gaza, da kuma ‘yan kasarsa da kungiyar Hamas ke garkuwa dasu, yana mai kira ga kungiyar data yi saranda ta saki mutanen idan tana son a kawo karshen yakin.

Firaministan na Isra’ila ya yi ta yaba yakin da kasarsa ke yi kan Hamas kusan shekaru biyu.

Ya kuma caccaki gwamnatocin kasashen yammacin duniya dake ci gaba da amincewa da falasdinu a matsayin kasa.

A nata bangare Kungiyar Hamas ta bayyana ficewar jam’ian difloamtaiyan daga zauren na MDD gabanin jawabin na Netanyahu da yadda duniya ta yi tir da kisan kare dangin Isra’ilar a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments