Venuzuwela Ta Kaddamar Da Atisayan Soji Don Mayar Da Martani Ga Barazanar Amuka

Shugaban kasar Venuzuwla Nicolas Maduro ya kaddamar da atisayan soji mai fadi, a jiya laraba, a daidai lokacin da rikici ke kara Kamari tsakaninsa da

Shugaban kasar Venuzuwla Nicolas Maduro ya kaddamar da atisayan soji mai fadi, a jiya laraba, a daidai lokacin da rikici ke kara Kamari tsakaninsa da Amurka, kuma an gudanar da atisayan ne a jihar coast a la guara, minti 30 da birnin karakas ,kuma ya kunshi sojojin kasar da hadin guiwar na kasar Bloviya.

Wannan Atisayan yana nuna irin karfin sojin da venuzuala take da shi da kuma shiri na tunkarar  barazanar da take fuskanta daga waje, kuma yana nuna irin yadda yankin karebiya ke cikin rikici inda ayyukan sojin ruwan Amurka ke fuskantar suka daga gwamnatin karakas.

Dangantaka tsakanin venuzuwela da Amurka ta dade da samun damuwa na tsawon shekaru,inda Amurka ta kakaba mata takunkumi kuma take goyon bayan kungiyoyin adawa a kasar, sai dai kasar venuzual na zargin Amurka da kokarin canja gwamnatin, ta hanyar soji da kuma matsin lambar tattalin Arziki,

A lokacin Atisayin venuzuwal ta gwada jirgin yaki kirar su-30 kuma ya harba bama bamai a inda ake so, dake kara tabbatar da shirin na tunkurar duk wata barazana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments