Venezuela ta yi Allah-wadai da Amurka kan abinda ta danganta da yakin da ba ta shelanta ba a yankin Caribbean, ta kuma bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta binciki sabon harin da Amurka ta kai kan wani jirgin ruwa, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku..
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa sojojin Amurka sun kai hari na uku kan wani jirgin ruwa da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi. Ya fitar da wani sabon faifan bidiyo da ke nuna abin da ya yi ikirarin harin da Amurka ta kai da ya kashe ‘yan ta’adda uku..
Wadannan hare-haren da jiragen yakin Amurka F-35 suka kai, rahotanni sun ce sun kashe akalla mutane 17 a cikin ‘yan makonnin nan.
Babban mai shigar da kara na Venezuela Tarek William Saab, ya ce harba makami mai linzami kan masunta marasa tsaro a cikin wani karamin kwale-kwale ya yi daidai da laifuffukan cin zarafin bil adama kuma dole ne Majalisar Dinkin Duniya ta yi bincike.