Hukumomin tsaro a kasar Venezuela sun kama wasu tarin bama-bamai a gabashin birnin Maturin na jihar Monagas, a wani abin da jami’ai suka bayyana a matsayin yunkurin da wasu bangarori masu tsatsauran ra’ayi suka yi na kai hare-haren ta’addanci da nufin kawo cikas ga gwamnatin shugaba Nicolas Maduro.
Ministan harkokin cikin gida, Diosdado Cabello, ya sanar a jiya Asabar cewa, jami’an tsaro, bayan gudanar da ayyukan leken asiri, sun gano wasu kayyayakin fashewa da abubuwan harhada bama-bamai da aka boye a wasu shaguna biyu.
Kayan sun dai sun hada da akwatuna 1,137 da ke dauke da wasu nauyin bama-bamai da ba a taba ganin irinsu a kasar ba, da rokoki 35, da igiyoyin tayar ta bama-bamai da ababen fashewa, na’urorin kashe wutar lantarki 125, na’urorin caji, wayoyin salula, da kwantena mai tsawon mita 60 mai dauke da manyan bama-bamai kamar C4.
Cabello ya tabbatar da cewa kawo yanzu an kama mutane takwas, dukkansu suna da alaka da kungiyoyin da ke adawa da kuma neman kawo cikas a kasar karkashin jagorancin ‘yar siyasa mai gudun hijira Maria Corina Machado. Haka kuma hukumomi na neman wasu mutane 10 zuwa 12 da hukumomin tsaro suka gano cewa suna da hannu dumu-dumu a cikin lamarin.