UNRWA : ba wani abu dake shiga Gaza in banda bama-bamai

Hukumar Ba da Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu a Gabas ta Tsakiya (UNRWA) ta yi gargadin cewa akwai

Hukumar Ba da Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu a Gabas ta Tsakiya (UNRWA) ta yi gargadin cewa akwai yiyuwar Gaza ta fuskanci matsalar jin kai mafi muni tun watan Oktoban 2023.

A cikin wani sako da ta wallafa a shafin X, UNRWA ta ce yanzu haka makonni 11 kenan da gwamnatin Isra’ila ta hana shigar da abinci, man fetur da magunguna zuwa Gaza.

“Makonni 11, jami’an Isra’ila da gangan sun hana duk wani kayan agaji zuwa Gaza, abin da kawai ke shiga Gaza a yanzu shi ne bama-bamai.

Daruruwan Falasdinawa ne aka kashe a wannan makon yayin da gwamnatin Isra’ila ke kara kai hare-hare ta sama, in ji UNRWA.

“Zafafa hare-haren bama-bamai ta sama da kasa da na ruwa na Isra’ila ya haifar da asarar daruruwan rayuka da kuma gudun hijirar jama’a.”inji hukumar

Mataimakin sakatare mai kula da harkokin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher ya fada jiya talata cewa jarirai 14,000 a Gaza za su iya mutuwa cikin sa’o’i 48 masu zuwa idan ba a kai musu dauki ba.

Tom Fletcher ya yi Allah-wadai da dokar hana kai kayan agaji zuwa zirin Gaza, yana mai cewa tireloli biyar ne kawai aka ba da izinin shiga a ranar Litinin, wanda ya bayyana a matsayin “digo a cikin teku.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments