Hukumar ci gaban kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ta fitar da wani rahoto dake cewa an ruguza fiye da kashi 80 cikin 100 na gine-ginen zirin Gaza.
UNDP ta ce, a Gaza kadai an lalata fiye kashi 92 cikin 100 na gine-ginen birnin.
Kakakin hukumar ya bayyana rugujewar gine-ginen da ”mummuna”,inda ta kiyasta cewa akwai akalla tan miliyan 55 na baraguzai da ke bukatar sharewa a yankin.
UNDP ta ce tuni ta fara aikin share baraguzan yankin, amma barazanar abubuwan fashewa da aka binne na kawo musu cikas a aikin.
Hukumar ta kara da cewa akwai gawarwakin mutane da ake ta tonowa yayin aikin.
Majalisar Dinkin Duniya da Bankin Duniya da kungiyar Tarayyar Turai sun kiyasta bukatar dala biliyan 70 domin sake gina Gaza.
shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyib Erdogan dake cikin shugabannin da suka ratabba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza ya ce ya yi imanin cewa za a samar da kudin sake gina Gaza.