Uganda Ta Sanar Da Kawo Karshen Ebola Da Ta Barke A Kasar

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Uganda ta sanar da cewa, an kawo karshen Ebola da ta bulla a kasar bayan da aka dauki kwanaki 42

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Uganda ta sanar da cewa, an kawo karshen Ebola da ta bulla a kasar bayan da aka dauki kwanaki 42 ba tare da an sami mutum daya wanda ya sake kamuwa  da ita ba.

 A wani bayani da ya fito daga hukumar kiwon lafiya ta duniya ( WHO), ta bayyana cewa, a lokacin bullar cutar an  gabatar da mutane 14 masu dauke da ita, an tabbatar da 12 daga cikinsu, sai wasu biyu da ba a same ta a tare da su ba.”

Haka nan kuma hukumar lafiyar ta ce, an sami mutuwar mutane 4 daga cikin wadanda su ka kamu da cutar ta Ebola, wasu mutane 10 kuma sun warke.”

Watanni 9 da su ka gabata ne dai aka tabbatar da bullar cutar a birnin Kamfala bayan da wani mutum da yake dauke da ita ya rasu.

Dajukan da kasar ta Uganda take da su, suna a matsayin matattarar cutar ta Ebola ce, wacce a karon farko ta bulla a cikin kasar a 2000.

A yankin yammacin Afirka cutar Ebola ta kashe fiye da mutane 11,000 a tsakanin 2013 zuwa 2016.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments