Sudan ta katse  hulda da Hadaddiyar Daular Larabawa bisa goyon bayan dakarun RSF

Gwamnatin Sudan ta katse dangantakar diflomasiyya da (UAE), bisa zarginta da goyan bayan dakarun RSF. A cikin jawabin da aka watsa a talabijin, Ministan Tsaron

Gwamnatin Sudan ta katse dangantakar diflomasiyya da (UAE), bisa zarginta da goyan bayan dakarun RSF.

A cikin jawabin da aka watsa a talabijin, Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye jakadanta da rufe ofishin jakadanci da konsulat dinta a kasar .

Da yake magana a gidan talabijin na gwamnatin kasa, ministan tsaron Sudan, Yassin Ibrahim Yassin, ya zargi Abu Dhabi da keta hurumin ‘yancin Sudan ta hanyar mara baya ta fuskar soji ga RSF, ciki har da samar da makamai, da jiragen yaki marasa matuka, da makamai masu linzami wadanda aka kai hari da su a baya-bayan nan a tashar jiragen ruwa, da filin jiragen sama, da kuma tashoshin wutar lantarki na Sudan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments