Search
Close this search box.

Turkiyya Ta La’anci Harin Isra’ila Kan Sansanin Nuseirat

Gwamnatin Turkiyya ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar zirin Gaza, wanda

Gwamnatin Turkiyya ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar zirin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da 200 tare da jikkata wasu daruruwa.

A wata sanarwa data fitar yau Lahadi, Ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta ce: “Muna matukar takaicin harin da Isra’ila ta kai kan sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke Gaza, wanda ya kashe daruruwan Falasdinawa.

Ma’aikatar diflomasiyyar Turkiyya ta bayyana wannan harin a matsayin “babban laifi” ta kara da cewa wannan harin ya bi sahun jerin laifukan yaki da Isra’ila ta aikata a Gaza.

“Muna kira ga cibiyoyin da ke da alhakin wanzar da zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, musamman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, da su yi amfani da alhakin da ya rataya a wuyansu na kawo karshen aikata wadannan laifuffuka da Isra’ila ke yi,”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments