An yi zaman farko na tattaunawar sulhu a tsakanin kasashen Habasha da Somaliya a birnin Ankara wanda kasar Turkiya take a matsayin mai shiga tsakani.
Ministan harkokin wajen kasar Turkiya Hakan fidan ya yi ganawa da daban-daban da ministocin harkokin wajen kasashen na Habasha da Somaliya.
Bayan wannan ganawar minstan harkokin wajen na Turkiya ya bayyana cewa; Yin aiki tare a tsakanin kasashen yankin yana da matukar muhimmanci a wannan zamanin da duniya take cike da sarkakiya.” Haka na kuma ya kara da cewa: Kai wa ga nasara a wannan tattaunawar yana da matukar muhimmanci fiye da kowane lokaci a baya.
Kamfanin dillancin labarun “Anatol” na Turkiya ya nakalto ministan harkokin wajen kasar yana yin ishara da babbar dama da aka samu a wannan lokacin domin ayyana makomar yankin na zirin Afirka, da kuma mayar da kalubalen da ake fuskanta ya zama wata dama
Minista Fidan ya kuma ce, tattaunawar da ake yi ba za ta takaita akan warare sabanin da yake a tsakanin kasashen na Habasha da Somaliya ba, zai zama mai wakiltar mahanga faffada ta siyasar nahiyar Afirka baki daya.