Tunisiya : Kaïs Saïed, ya kori firaministansa Kamel Madouri

Shugaba Kaïs Saïed na Tunisiya ya kori firaministan kasar Kamel Madouri,  da aka nada a watan Agustan da ya gabata yayin wani gagarumin garanbawul a

Shugaba Kaïs Saïed na Tunisiya ya kori firaministan kasar Kamel Madouri,  da aka nada a watan Agustan da ya gabata yayin wani gagarumin garanbawul a majalisar ministocin kasar a daren jiya Alhamis.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce an maye gurbin firaministan kasar Madouri nan take inda aka maye gurbinsa da Sarra Zaafrani Zenzri, ministar kayan aiki.

Sanarwar ta ce sauren mambobin gwamnatin zasu ci gaba da aikinsu.

Garan bawul na shugaban kasar ta Tunisia a baya baya nan shi ne na ranar 6 ga watan Fabrairu inda ya sallami ministan kudinsa Sihem Boughdiri Nemsia da tsakar dare, tare da maye gurbinsa da alkalin kotun Michket Slama Khaldi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments