Kafafen watsa labarun kasar ta Zambia da kuma jam’iyyarsa ta “PFT” sun sanar da cewa; Tsohon shugaban kasar ya fadi ne a lokacin da yake motsa jiki a gidansa dake birnin Lusaka. Bayan da aka kai shi asibitin soja na “Maina Soko” likitoci sun tabbatar da cewa ya rasu.
Gwamnatin kasar ta Zambia ta tabbatar da rasuwar tsohon shugaban kasar, tare kuma da shelanta ranakun alhini na kasa.
Shi dai Lunga ya jagorancin kasar ta Zambia ne daga 2015 zuwa 2021 da ake yabonsa da gina muhimman cibiyoyi a kasar, sai dai kuma hakan ya bar kasar da dimbin bashi.
Ya zuwa yanzu dai ba a sanar da lokacin da za a yi jana’izar tsohon shugaban kasar ba.