Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar rage kudaden da gwamnatin tarayya ke ba wa kwalejoji da jami’o’in da ke ba da izinin ” zanga-zangar goyan bayan Falasdinawa tare da hukunta daliban da suka shiga irin wannan zanga zanga.
Trump ya yi wannan gargadin ne a wani sako da ya wallafa a dandalinsa na sada zumunta bayan da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa suka taru a harabar jami’ar Columbia da ke New York.
Shugaban na Amurka ya kara da cewa “za a daure masu tayar da hankali” ko dai a daure su ko kuma a tura su dindindin zuwa kasashensu na asali.”
Ko da yake bai ambaci musamman zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a cikin sakon nasa ba, amma a baya Trump ya yi barazanar korar duk daliban da suka shiga zanga-zangar adawa da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a zirin Gaza.
A karshen watan Janairu, Trump ya rattaba hannu kan wata doka da ta bukaci gwamnati ta kori daliban kasashen waje da suka shiga zanga-zangar goyon bayan Falasdinu.
Ya yi zargin cewa zanga-zangar da aka yi a harabar jami’ar ta haifar da “kyama, barna da kuma cin zarafi a kan ‘yan kasarmu, musamman a makarantunmu da harabar jami’armu.”
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da masana shari’a sun dage cewa wannan umarni ya saba wa ‘yancin fadin albarkacin baki da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.