Gwamnatin Donald Trump ta kawo karshen wani shirin Amurka na bunkasa samar da wutar lantarki a Afirka, wanda aka kaddamar fiye da shekaru 10, in ji Bloomberg.
Shirin wanda tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya kaddamar a shekarar 2013, yana da nufin samar da wutar lantarki ga miliyoyin gidaje a nahiyar Afirka, wanda Hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) ke tafiyar da shi.
Wannan na daga cikin shirin Trump na rage kashe kudade na tarayya wanda ma’aikatar ingancin gwamnati ke jagoranta.
Kusan dukkanin manufofin shirin “Power Africa” an sanya su cikin jerin shirye-shiryen da za a kawar da su.
A ranar 20 ga watan Janairu, ne shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka ta dakatar da tallafin da Amurka ke bayarwa, wanda kungiyoyi masu zaman kansu da dama suka dogara da da shi.