Shugaban kasar Amurka Donal Trump a tattaunawa ta wayar tarho da firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya bukace shi ya daina shiha a cikin tattaunawar da Amurka take da JMI. Kafin haka dai firai ministan ya sha barazanar kai hare-hare kan cibiyoyin nukliyar kasar Iran a dai-dai lokacinda ake tattaunawar. Wanda kuma yake tasiri a cikin abubuwan da ake tattaunawa tsakanin kasashen biyu.
Sishshigin da HKI suna zama manya-manyan labarai a kafafen yada labarai na duniya, wanda kuma yakan sa JMI ta maida martani. Don haka kutsawar da HKI take yi yana rikita tattaunawar, wasu suna fadar cewa HKI ce take fadar abinda wakilin Amurka zai fada a tattaunawar.
Ya zuwa yanzu dai Washington da Tel Aviv suna da sabanin kan yadda zasu yi mu’amala da iran a wannan tattaunawar. HKI bata son a yarjewa kasar Iran ta tashe Makamashin Uranium ko kadan. A yayinda Amurka kuma tana son ta tabbatar da